Hollande ya bayyana matsayinsa game da Rasha
Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande yace babu wanda zai hura masa wuta wajen bai wa kasar Rasha jiragen ruwan dake daukar jiragen yakin da ta saya daga hannun kasar. Shugaba Hollande ya bayyana matsayin sa ne kan cinikin jiragen ruwan tsakanin Faransa da Rasha a wajen taron G20 da aka kammala a kasar Australia inda ya ke cewar shi ke da wuka da nama wajen amincewa da mika jiragen, kuma babu wanda zai tilasta ma sa daukar mataki akai.
Wallafawa ranar:
Hollande yace ya zuwa yanzu Faransa ba ta karya yarjejeniyar kwangila da aka kulla ba wadda ta kunshi mikawa Rasha jirage a karshen wannan wata.
Amurka da sauran kasashen Turai na matsawa Faransa lamba wajen ganin ta ki mika jiragen har sai Rasha ta sanya hannu wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Ukraine.
Shugaban Rasha Vldamir Putin ya bukaci Hollande ya kaucewa karya alkawarin da kasashen biyu suka kulla, inda yace suna da shirin daukar mataki akai.
An dai kulla yarjejeniyar kwangilar ta Dala biliyan daya da rabi ne a karkashin shugabancin Nicolas Sarkozy, kuma ko a karshen mako Sarkozy ya yi kira ga Hollande da ya mutunta kwangilar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu