Isa ga babban shafi
Rasha-Syria-Amurka

Rasha ta gargadi Amurka akan Syria

Gwamnatin kasar Rasha tace hare haren Jiragen yaki da Amurka tace zata kaddamar akan Mayakan IS a Syria mataki ne da ya keta dokokin duniya. Amurka zata kaddamar da hare haren ne ba tare da tuntubar Syria ba ko amincewar kwamitin sulhu, a cewar Rasha.

Shugaban Rasha  Vladimir Putin da takwaransa na China Xi Jinping a wata ganawa da suka yi a taron Shanghai
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na China Xi Jinping a wata ganawa da suka yi a taron Shanghai REUTERS/Mikhail Klimentyev/RIA Novosti/Kremlin
Talla

A kafar Telebijin, Mai magana da yawun Ma’aikatar harakokin wajen Rasha, Alexander Lukashevich yace matakin da Amurka ta kaddamar ya sabawa dokokin duniya.

A ranar Laraba ne Shugaban Barack Obama yace a shirye Amurka ta ke ta kaddamar da hare hare ta sama akan Mayakan IS da suka mamaye wani yanki na Syria bayan kaddamar da hare haren a Iraqi.

Amma Rasha ta soki matakin a matsayin wani zagon kasa saboda yadda Amurka ta fito karara tana goyon bayan ‘Yan tawayen Syria da ke fada da Bashar Al Assad.

Kasar Birtaniya tace ba za ta bi sahun Amurka ba wajen kai hare hare da jiragen sama akan Mayakan Jihadi da ke fada Syria da iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.