Faransa tace ba gudu ba ja da baya a yaki da ta'addanci
Shugaban Faransa Francois Hollande yace ba gudu ba ja da baya, wajen yaki da ayyukan ta’addanci. Shugaban ya fadi hakan ne a gaban majalisar dokokin Canada, a lokacin daya kai ziyara a kasar.Shugaba Hollande dake jawabi a gaban majalisar dokokin kasar ta Canada, inda wani dan bindiga ya kai wa hari kusan makonni 2 da suka gabata, yace gamaiyyar kasashen duniya ba zasu yi kasa a gwiwa ba, a yakin da suke yi da ayyukan ta’adanci.Mr. Hollande yace ta’addanci na barazana ga ginshikin da aka kafa kasashen Faransa da Canada a kai, don haka a cewar shugaban, dole a tashi tsaye.Ya kuma yi bayani kan yadda kasashen 2 suka bi sawun sauran kasashen duniya dake ci gaba da kai hare ta sama kan mayakan kungiyar IS a Iraai, inda yace suna aiki tare don sauke nauyin da aka dora musu.A ranar 22 ga watan Oktoban daya gabata, wani dan bindiga ya kai hari a majalisar dokokin kasar ta Canada, dake birnin Ottawa, inda ya harbi wani soja dake gandi a kusa da ginin, kafin daga bisani ‘yan sanda suka bindige maharin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: