Isa ga babban shafi
Britaniya

Kotun Britaniya ta yake wa tsohon editan jaridar News of The hukuncin dauri

Wata kotun kasar Britaniya ta yake wa tsohon Editan jaridar News Of The World Andy Coulson, hukuncin daurin watanni 18 a gidan kaso, saboda rawar da ya taka a badakalar nan ta sauraren sakonnin wayoyin hannun jama’a. Wannan hukuncin ne ya kawo karshen tashen Coulson mai shekaru 46, daya taba zama na hannun daman Prime Minister david Cameron.Akwai wasu abokan aikin Coulson a kamfanin Jaridar, wadda dama aka rufe ta, da suma aka yanke musu hukuncin da bai kai nashi ba, saboda rawar da suka taka a badakalar ta sauraron sakonnin wayoyin dubun dubatar ‘yan kasar, da suka hada da ‘yan gidan sarauta, mashahuran mutane da ma ‘yan siyasan kasar. 

Tsohon editan jaridar News of the world, Andy Coulson,
Tsohon editan jaridar News of the world, Andy Coulson, REUTERS/Neil Hall
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.