Isa ga babban shafi
Google

Turawa 70,000 ke bukatar Google ya share bayanansu

Babban kamfanin Bincike na Intanet Google, ya ce sama da mutane dubu saba’in ne dukkaninsu daga nahiyar Turai suka gabatar masa da bukatar ganin cewa an shafe bayansu daga taswirar bincike a Intanet.

Shafin bincike na Google a Intanet
Shafin bincike na Google a Intanet @Google
Talla

Tun a ranar 30 ga watan Mayun da ya gabata ne Google ya bayyana aniyarsa ta shafe irin wadannan bayanai kamar dai yadda Kotun Tarayyar Turai ta bukaci a yi saboda dalilai na sirri.

Bayan da kotun Turai ta yanke hukuncin, google ya bude shafi domin ba masu bukatar a share bayanansu damar aikawa da bukatunsu tare da cika wasu sharudda da kamfanin ya shata.

Google yace yana samun bukatar daga mutanen na Turai a cikin kowace dakika bakwai, musamman daga ‘yan siyasa da wadanda ke son a dakile hoto ko bidiyonsu na tsaraici.

A watan Mayu ne kotun Turai ta yanke hukunci akan mutane suna da ‘Yancin a share wasu bayanan da ba su bukata musamman tsuffin bayanansu a intanet. Sai dai masana suna ganin wannan zai haifar da cikas ga ‘yancin samun bayanai musamman ga aikin bincike na Jarida.

Wannnan mataki dai ya shafi yankin Nahiyar Turai ne musamman kokarin kare mutunci mutanen Nahiyar a internet. Amma wata kila kuma wasu mutanen ketare zasu iya samun bayanan da google ya toshe a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.