Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya kaddamar da bikin tuna yakin Duniya shekaru 100

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, a yammacin Alhamis ya kaddamar bukukuwan soma tunawa da cika shekaru 100 da kaddamar da yakin duniya na daya wanda aka fara daga shekarar 1914-1918.

Shugaban Faransa François Hollande
Shugaban Faransa François Hollande FranceTV/capture d'écran
Talla

Sai dai shugaban na Faransa ya fi mayar da hankali ne dangane da wasu sojojin kasar 740 da aka harbe bainar jama’a, bayan da aka same da su yunkurin tserewa daga fagen daga, lamarin da har yanzu yake ci gaba da raba kawunan al’ummar kasar,

A cikin Jawabin Hollande, shugaban yace ba wani dan kasar Faransa da ya rasa rayuwarsa a wannan lamari na assha da za a manta da shi, saboda haka ne ma ya bukaci ministan tsaro, da ya samar da sashe na musamman a cikin gidan ajiye kayayyakin tarihi da na sojin Faransa domin tunawa da wadannan mutane.

Shugaban ya kuma bukaci a gaggauta fitar da kundi mai dauke da cikakkun bayanai dangane da yake-yaken da suka taba faruwa a can baya domin jama’a su san da zamansa.

Hollande yace yanzu ba lokacin da za a ci gaba da yin zargi ko kuma neman hukuntar da wani dangane da wannan batu ba ne, yace yanzu lokacin tunawa ne da abubuwan da suka faru a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.