Isa ga babban shafi
Faransa

Adadin mutanen da ke samun izinin zama 'Yan Faransa ya karu

Yawan wadanda aka bai wa takardun zama yan kasar Fransa ya karu ainun, tun zuwan jam’iyar gurguzu a kan karagar mulkin kasar, sakamakon yadda gwamnatin kasar ta bai wa lamarin muhimmanci, wanda ya kawo karshen tsarin da gwamnatin da ta gabata ta Nicolas Sarkozi ke bi wajen bai wa yan kasashen waje takardun zama yan kasar.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande Reuters/路透社
Talla

Daga watan Yulin 2012 zuwa Yulin 2013 an bai wa kimanin kashi 14 cikin dari na baki yan kasashen waje takardun zama ‘yan kasar ta Faransa, fiye da na shekarar da ta gabata kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Faransa Najat Vallaud Belkasem wace ita ma asalinta bakuwa ce ta sanar.

Bayanai sun nuna cewa, ko ministan cikin gidan kasar Faransa Manuel Val bako dan kasar Spain, ya kuma zama dan kasar Faransa yana dan shekaru 20 a duniya a 2081.

Haka kuma shigarsa gwamnatin Faransa ya saukaka hanyar samun takardun zama dan kasar.

Umarnin farko da gwamnatin Faransa ta bai wa kananan hukumomin kasar, shi ne su kara yawan damar da suke bai wa masu neman takardun zama ‘yan kasar daga kashi 40 cikin dari 2011 zuwa kashi 60 cikin dari a wannan lokaci da muke ciki, kamar yadda sakamakon hukumomi kasar ya nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.