Isa ga babban shafi
Faransa

Matsalar tsarin Fansho a Faransa

Firaministan kasar Faransa Jean Marc Ayrault, ya yi wata ganawa da kungiyoyin kwadago da wasu kungiyoyin samar da ayyukan yi a kasar, akan batun samar da ingantancen tsarin Fansho wanda shi ne batu day a mamaye siyasar Faransa.

Firaministan Faransa  Jean-Marc Ayrault
Firaministan Faransa Jean-Marc Ayrault REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Taron ya mayar da hankali ne game da kudaden fanshon ma’aikatan kasar kuma hakan na da nasaba da yunkurin da gwamnatin Faransa ke yi na rage gibin da kasar ta samu wajen biyan kudaden na fansho.

Ana sa ran gwamnatin Francois Hollande za ta baje tsare-tsaren da ta shirya game da biyan kudaden na fansho, wanda masana ke hasashen zai haura zuwa biliyan 20 na euro nan da zuwa shekarar 2020 muddin ba a dauki mataki ba.

Wani batu kuma da ake sa ran zai kunno kai shi ne batun kara yawan shekarun yin ritaya a aiki daga shekaru 62 zuwa sama wanda tsohon shugaba, Nicolas Sarkozy ya kara daga shekaru 60 zuwa 62.

Batun ritaya a kasar Faransa batu ne da kan dauki hankulan jama’a da dama domin bincike na nuna cewa adadin mutane masu yawan shekaru na karuwa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.