Isa ga babban shafi
Switzerland

Babban bankin Switzerland na UBS na gudanar da garanbawul

Hukumar dake sa idanu kan harkokin bankuna a kasar Switzerland ta umarci babban bankin kasar UBS da ya ware wasu kudade masu kauri domin tunkarar matsalolin kararraki dakan biyo bayan gagarumi garambawul da harkan bankunan kasar ke fuskanta.

Tambarin babban bankin Switzerland na UBS
Tambarin babban bankin Switzerland na UBS ©Reuters / Michael Buholzer
Talla

Hukumar dake sa idanu kan bankunan kasar FINMA, na cewa Bankin wanda ya ke cikin rudani, na fuskantar gagarumin sauye-sauye ne yanzu haka, na cewa umarnin ya zama wajibi saboda a yi dukkan wani abin da zai biyo baya, idan aka yi la’akari da abubuwan da suka faru dan tsakanin nan.

Saboda haka Bankin ya ce daga watanni hudu masu kamawa na wannan shekarar, za ta kara yawan wani kaso don fuskantar dukkan wata matsala, inda za a kara zuba kudin daya kai kudin Amurka Dala biliyan sama da 31.

Sakamakon haka in ji hukumar za a kara yawan kudaden dake hannun bankin ke nan.

Hukumar kula da harkokin bankunan kasar ta Switzerland ba su ce jerin wadannan matakai nada nasaba da kaddamar da binciken data nemi a yi ba farkon wannan wata, saboda zargin babban bankin kasar ya karya dokokin aikin sa.

Shi dai babban bankin kasar Switzerland na aiwatar da gagarumin garambawul ne inda har aka rage ma'aikata akalla dubu 10 da kuma gyatta lamurransa a idanun duniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.