Isa ga babban shafi
Turai

Ruwan sama da iska mai karfi sun yi ta'adi a Turai

Ruwan sama gami dauke da isaka mai karfin gaske, da suka shafi yankin arewacin nahiyar Turai a jiya litanin sun yi sanadiyar hasarar rayukan akalla mutane 8, a yayin da sama da gidaje dubu 340 suka rasa wutar lantarkiKasar ta Britaniya ce kasar da iskan dake tafe da ruwan saman ta fi yiwa illa, inda aka bayyana cewa mutane 4 ne suka rasa rayukansu, kuma iskar ce mafi muni da kasar ta gani a cikin shekaru 5 da suka gabata, Lamarin ya haifar da tsayawar zirganiyar ababen hawa tare da lalata wayoyin wutar lantarkiHar ila yau ruwan hade da iska sun yi sanadiyar mutwar mutum guda a kasar Fransa, biyu a Jamus a yayinda kasar Holande ta rasa mutum gudaBaya ga barnar da wannan ruwa dake tafe da iska suka haddasa wa motoci da rufin gidaje sakamakon itacen da iskar ta tumbuke suka fada masu, har ila yau harakokin sufuri jiragen kasa da na sama da ruwa duk sun tsaya cak a jiyaTun a makon daya gabata ne hukumar dake kula da hasashen yanayi ta nahiyar Turai Met Office, ta bayyana hango wani dunkulen iska mai gudun kilo mita 160 a sa’a daya, ya doso kudancin tsibirin Wight, wanda ya sa ta tsananta gargadi ga kasashen na arewacin Turai, game da hadarin.  

Yadda na'urar tauraron dan Adam ke daukar hoton guguwa
Yadda na'urar tauraron dan Adam ke daukar hoton guguwa REUTERS/NOAA/GOES East/Handout
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.