Ba za a taba filin shakatawa na Gezi ba sai da amincewar kotun Turkiyya
Firayi ministan Turkiyya Racep tayyip Erdogon ya bukaci masu Zanga-zanga da su fice daga dandalin Taksim tare da daukar alkawalin cewa ba za a gudanar da aikin sake fasalta filin shakatawa na Gezi ba sai zuwa lokacin da kotu ta yanke hukunci a game da karar da masu adawa da shirin suka shigar a gabanta.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tuni dai Erdogan ya gana da shugabannin masu zanga-zangar domin sasantawa amma wasu daga cikinsu sun ce babu wani sasantawa saboda yadda aka yi amfani da karfi wajen murkushe su.
A kalamansa na baya bayan nan, Erdogon ya ce idan dai saboda aikin sake fasalta dandanlin shakatawa na Gezi ne suke zanga-zanga, to a yau ba bu hujjar ci gaba da yin tarzoma a kasar, domin kuwa gwamnatinsa ta dakatar da shirin sai bayan kotu ta yanke hukunci a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu