Isa ga babban shafi
Turkiya

Mummunan artabu tsakanin jami'an tsaro da masu tarzoma a Turkiyya

Jami’an tsaro sun yi nasarar kutsa kai dandalin Taksim, inda masu zanga ke ci gaba da adawa da manufofin Firaminista, Recep Tayyip Erdogan. Rahotanni sun ce Jami’an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi domin tarwatsa masu zanga-zanga.

'Yan sanda suna kutsa kai a Dandalin Taksim da masu zanga-zanga suka mamaye a Istanbul
'Yan sanda suna kutsa kai a Dandalin Taksim da masu zanga-zanga suka mamaye a Istanbul REUTERS/Osman Orsal
Talla

Wannan kuma na zuwa ne bayan Erdogan ya amince a karon farko zai gana da shugabanin masu zanga zangar a gobe laraba.

Daruruwan ‘Yan sanda ne suka kutsa kai a dandalin bayan sun fice a ranar 1 ga Juni.
A ranar litinin dubban masu zanga-zanga ne suka mamaye titunan biranen Istanbul da Ankara, suna masu bijirewa gargadin da Erdogan ya yi na daukar mataki akansu.

Zangar-zangar Turkiya dai ta barke ne a ranar 31 ga watan Mayu, inda ‘Yan sanda suka tarwatsa gungun masu yakin neman kare wani wurin shakwata da ake kira Gezi Park da gwamnatin Erdogan zata wargaza da ke kusa da dandalin Taksim.

Wannan matakin ne kuma ya rikide zuwa zanga-zangar kin jinin Jam’iyyar AKP mai mulki ta Firaminista Erdogan, inda masu zanga-zangar suka nemi lalle a gaggauta gudanar da zabe domin samun sauyin gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.