Isa ga babban shafi
Turkiya

Ba za mu mika wuya ga masu bore ba - Erdogan

Firaminstan Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ya yi kiran kawo karshen zanga zangar da aka kwashe sama da mako guda ana yi dan adawa da Gwamnatinsa, inda ya bukaci dubban magoya bayansa da suka tarbe shi lokacin da ya koma kasar da su koma gidajensu.

Firaministan kasar Turkiya, Tayyip Erdogan, a lokacin da yake bayani ga magoya bayansa
Firaministan kasar Turkiya, Tayyip Erdogan, a lokacin da yake bayani ga magoya bayansa REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Dubban magoya bayan Erdogan ne suka yi dafifi dan tarbar sa lokacin da ya koma kasar, inda suke rike ta tutocin kasar, kuma suke bayyana cewar a shirye suke su mutu domin sa.

A jawabin da ya yiwa taron magoyan bayansa, Erdogan ya bukaci kawo karshen zanga zangar da ake a cikin kasar, wanda ya danganta ta da wadanda suka rasa halarcin shaidarsu ta demokradiya, inda ya kuma umurci masu goya masa baya da su koma gidajen su.

Firaministan ya kuma yabawa magoya bayansa kan yadda suka gudanar da ganganmin su ba tare da tada hankali ba, inda ya shaida musu cewar zaben sa akayi, saboda haka ta hanyar zabe ne kawai zai bar karagar mulki.

Erdogan ya kuma ce zai cigaba da aikin gine ginen da ya shirya a Instanbul a yayin da ya ke zargin cewa rikicin wanda ya lakume rayuka uku ciki har da na dan sanda, na da hanun wasu ‘Yan ta’adda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.