Isa ga babban shafi
Bulgaria

An nada sabon Piraiministan kasar Bulgariya.

Majalisar kasar Bulgaria, ta tabbatar da nadin sabon Piraiministan kasar. Wanda aka nada din dai, wani fitaccen masanin Tattalin arzikin kasa ne Plamen Oresharski, al’amarin daya kawo karshen ‘yar takaddamar da aka samu a wannan kasar dake sahun baya wajen tattalin arziki a kasashen Turai.

sofiaglobe.com
Talla

Wakilan majalisar kasar Dari daya da Ashirin ne suka amince da zabensa, daga cikin wakilai Dari biyu da Goma sha Bakwai, ma’ana kenan wakilai 97 suka nuna basa goyon bayan sa a matsayin sabon Piaraiminista.

Ba tare da jinkiri ba, aka rantsar da sabon Piraiministan da wakilan majalisar kasar domin fara aikin ba tareda bata lokaci ba.

Kasar ta Bulgariya dai na fama ne da manyan matsalolin tattalin arziki da tsadar Rayuwa.

Sabon Piraiministan mai shekaru 53 ya shaidawa Majalisar kasar kamin ayyanawa da kuma rantsar da shi a matsayin Praiminista, ya bayyanawa Majalisar cewar ba lallai ne kasar ta kasance mai dimbin Arziki sakamakon nadin da aka yimasa ba, amma kuma tareda damar da aka bashi zai yi kokarin ganin cewar akalla dukkanin ‘yan Bulgariya sun samu muhimman kayan more Rayuwar su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.