Isa ga babban shafi
Birtaniya

'Yan adawa sun yi nasara a zaben da aka gudanar a Iceland

Jam’iyyar adawa ta masu tsaka-tsakan ra’ayi a kasar Iceland, ta soma tattaunawa da sauran jam’iyyun adawa na kasar domin kafa sabuwar gwamnati, jim kadan bayan nasarar da ta sama a kan jam’iyyar da ke mulki ta Social Democrat a zaben da aka gudanar a kasar.

Pirami Ministan Iceland mai barin gado, Johanna Sigurdardottir
Pirami Ministan Iceland mai barin gado, Johanna Sigurdardottir
Talla

Wasu daga cikin alkawullan da jam’iyyar ta yi wa al’umma har ma ta samu wannan nasara, sun hada da dakatar da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati na tsawon shekaru biyar da gwamnatin da ta sha kaye ke kan aiwatarwa.
Sakamakon zaben dai, ya yi nuni da cewa jam’iyyar ta samu kashi 29,7 bisa dari, sai jam’iyyar Progressive Party wadda ta samu kashi 24,4 bisa, yayin da jam’iyyar da ke mulki ta zo a matsasyin ta uku da kashi 12,9 cikin dari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.