Isa ga babban shafi
Cyprus

Mutane da dama sun yi jerin gwano domin cirar kudi a bankunan Cyprus

An bude bankunan Cyprus amma mutane da dama ne suka yi jerin gwano a harabar bankunan domin cirar kudi bayan shafe kwanaki 12 bankunan na rufe. Amma akwai tsauraran matakai cirar kudi da gwamnatin kasar ta dauka bayan amincewa da yarjejeniyar kungiyar kasashen Turai.

jerin gwanon mutanen da ke neman cirar kudi a birnin Nicosia a kasar Cyprus
jerin gwanon mutanen da ke neman cirar kudi a birnin Nicosia a kasar Cyprus REUTERS/Andreas Manolis
Talla

Bayan shafe makwanni biyu bankunan Cyprus na rufe, gwamnatin kasar ta cim ma yarjejeniyar kudi euro Milian 10 daga kungiyar kasashen Turai.

Daruruwan mutane ne suka yi dandazo a harabar bankunan amma akwai adadin kudin da aka kayyade ga masu cirar kudi a bankunan.

Ma’aikatar kudin kasar ta kayyade adadin kudaden da mutum zai iya cira zuwa euro 300 a rana tare da haramta amfani da takardar karbar kudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.