Girka na samun matsin lambar kare turbar demokradiya
Kasar Girka na samun matsin lamba daga kwamitin kungiyar Nahiyar Turai kan kare turbar demokradiya a kasar a yayin da masu ra’ayin Nazi ke kawo barazana ga kasar. Kwamishinan kungiyar kare hakkin Bil adama a Nahiyar ta Turai, Nils Muiznieks ya bayyana hakan inda ya nemi da a yi maza-maza a magance matsalar tun yanzu.
Wallafawa ranar:
“Matsalar ita ce idan ba a magance matsalar yanzu ba, baza a iya magance ta nan gaba ba." Inji Muiznieks.
Wadannan kalamai na Muiznieks na zuwa ne bayan wata ziyarar kwanaki biyar da ya kai a kasar ta Girka domin yunkurin dakile matsalar wariyar launin fata, wadanda rahotanni suka nuna cewa an samu akalla guda 200 da aka kawo kara a tsakanin watan Oktoban shekarar 2011 zuwa watan Disambar shekarar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu