Isa ga babban shafi
Girka

An kai hari kan ofishin Jam’iya mai mulki a Girka

‘Yan sanda a kasar Girka sun tabbatar da kai hari kan ofishin Jam’iya mai mulki a kasar, New Democratic, a birnin Athens, inda harsashi ya bula bango ya shiga ofishin Firaministan kasar. Wasu mutane su biyu ne suka harbi akan ginin ofishin a wani yankin Athens da misalin karfe 2:30 na safiyar yau, sai dai rahotanni sun nuna cewa babu wanda ya samu rauni. 

Firaministan kasar Girka, Antonis Samaras
Firaministan kasar Girka, Antonis Samaras REUTERS/Yorgos Karahalis
Talla

Wani mai daukan hoton Kamfanin Dillancin labaran AFP, ya tabbatar da cewa harsashi ya bula tagar ofishin Firaministan kasar, Antonis Samaras.

“Bazu mu bari, a dinga yi mana barazana ba, gwamnati zata yi duk abinda ya dace ta yi, domin kare turbar demokradiya.” Inji Mai Magana da yawun, Samaras.

Sai dai rahotanni na nuna cewa babu wanda aka kama bayan harin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.