Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta nemi ‘Yan majalisunta su marawa Girka baya

Ministan Kudin kasar Jamus ya yabawa yunkurin da kasar Girka ke yi na ganin cewa ta farfado da tattalin arzikinta a dai dai lokacin da ya nemi ‘Yan majalisun kasar har ila yau da su taimaka wajen ganin an amince da bawa kasar ta Girka taimakon kudi na biliyoyin Euro na kasa da kasa domin ta fice daga matsalar da take ciki. 

Ministan kudin kasar Jamus, Wolfgang Schaeuble
Ministan kudin kasar Jamus, Wolfgang Schaeuble REUTERS/Miguel Vidal
Talla

Wannan kira da Ministan kudin ya yi, Wolfgang Schaeuble, na zuwa ne a yayin da aka tunkari kada kuri’a majalisar ta Jamus.

A cewar Schaeuble, ceto tattalin arzikin kasar na Girka abu ne mai wuya mai kuma tsada, inda ya nuna muhimmancin amincewar ‘Yan majalisun a matsayin wani mataki da zai taimakawa kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.