Isa ga babban shafi
Birtaniya-Faransa

Birtaniya da Faransa sun amince da Gwamnatin ‘Yan tawayen Syria

Gwamnatin Birtaniya ta bi sahun Faransa da kungiyar kasashen Turai, wajen amincewa da ‘Yan Tawayen Syria, a matsayin wakilan al’ummar kasar. Sakataren harkokin wajen kasar, William Haque, ya bukaci ‘Yan Tawayen su kara kokari don samun goyan bayan daukacin al’ummar Syria.

W. Hague tare da M. Khatib
W. Hague tare da M. Khatib Reuters
Talla

Wannan na zuwan ne a dai dai lokacin da rikicin Syria ke ci gaba da lakume rayukan mutane.

A birnin Ras al-Ain an samu Rikici tsakanin dakarun Kurdawa da ‘Yan tawaye. Akan haka ne kuma Gwamnatin Turkiya da ke adawa da Bashar al Assad ke naman taimakon NATO don kare iyakokinta da Syria.

Kasar Faransa ita ce kasa ta farko daga kasashen Turai da ta amince da gwamnatin ‘Yan tawayen kafin kungiyar Tarayyar Turai ta amince da ‘Yan tawayen a ranar Litinin.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya yi kira ga kungiyoyin agaji su taimakawa ‘Yan gudun hijirar Syria da kayayyakin abinci wadanda suka gudu zuwa makwabtan kasashe daga Syria.

A ranar 12 ga watan Disemba ne kasashen da ke goyon bayan Gwamnatin ‘Yan tawaye za su gana a birninMarrakesh na kasar Morocco wadanda suka hada Hillary Clinton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.