Isa ga babban shafi
Turai

Yawan marasa aikin yi ya karu a kasashen Turai

Rashin ayyukan yi ya karu a yankin kasashen Nahiyar Turai masu amfani da kudin Euro da kashi 11.6 a watan Satumba, inda aka yi ikrarin karuwar batar guraban ayyukan sama da 150,000, a yayin da matsalar basussuka ke addabar yankin. Wannan dai shine karo na farko da wannan matsalar ta kai ga haka inda karuwan marasa ayyukan yi ada yake 11.5 a watan Agusta.  

Wata Bafaranshiya a Nahiyar Turai
Wata Bafaranshiya a Nahiyar Turai REUTERS/Christian Hartmann
Talla

A kasar Spain, inda akafi samun yawan karuwar rashin ayyukan yi da kashi 25.8, a yayin da Austria ta samu karin kashi 4.4, kana Jamus da Netherland suka samu karin marasa ayyukan yi da kashi 5.4.

Idan aka kwatanta yankin na Euro zone da kasashen dake hamayya dasu, kasara Amurka a ranar Juma’a ta bayyana karin marasa aikin yi da kashi 7.8 a watan Satumba a yayin da Japan ta bayyana karin kashi 4.2.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.