Isa ga babban shafi
Birtaniya-Sweden

Shafin Wikileaks ya yi Allah waddai da Birtaniya

Kasar Ecuador ta bada mafakan siyasa ga Julian Assange mutumin nan da ya yi kaurin suna saboda wallafa sirrin kasashen duniya a shafin yanar gizo na Wikileaks.  

Shugaban Shafin kwarmata bayanan Siri na WikiLeaks,  Julian Assange.
Shugaban Shafin kwarmata bayanan Siri na WikiLeaks, Julian Assange.
Talla

Julian Assange ya nemi mafaka ne a ofishin jakadancin kasar Ecuador dake Britania, domin ya gujewa tattara shi zuwa Sweden inda ake zargin sa da laifukan yin lalata da wata.

Ministan waje na kasar Ecuador Ricardo Patino ya shaidawa taron manema labarai dazun nan cewa, aladar kasar ita ta amince da bukatar mafakan siyasa ga mabukata, saboda haka ba za a hana Julian Assange ba.

a dai gefen kuma, Shafin Wikileaks da ke kwarmata bayanan sirri ta internet, ya yi Allah wadai da barazanar da hukumomin Britaniya suka yi na kai samame ofishin jakadancin Ecuador a London da cewa, nuna kiyayya ne da barazana ga masu neman mafakar siyasa.

Tun a watan Yuni, Wanda ya kirkiro shafin na Wikileaks Julian Assange ke ofishin jekadancin Ecaurdo, don gudun kada a mika shi Sweden, inda zai amsa tuhuma kan zargin aikata fyade.

Assange, dan kasar Australia, yana fargabar in aka kai shi Sweden, hukumomin kasar za su iya mika shi Amurka, inda ake zargin shi da leken asiri, da hada baki, saboda bayanan da shafin shi ya yi ta fitarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.