Isa ga babban shafi
Somaliya

Sojan Denmark sun ceto wadanda aka yi garkuwa dasu a ruwan Somaliya

Rindinar sojan ruwan kasar Denmark, ta kubutar da wasu matukan jiragen ruwa 16 da 'yan fashin ruwan Somalia suka yi garkuwa da su, yayin da biyu suka rasa rayukansu.  

AFP PHOTO/SPANISH MINISTRY OF DEFENCE HANDOUT
Talla

Rindinar ta ce ta kuma kama 'yan fashin 17, kamar yadda kakakin ta Kenneth Nielsen ya bayyana, yayin aikin ceton da suka kaddamar kan gaban ruwan kasar ta Somaliya.

Kasar ta Denmark tana cikin sojojin kungiyar NATO dake aikin kare jiragen ruwa daga barayin gaban ruwan Somaliya. Kasar ta Somaliya dake yankin Kahon Nahiyar Afrika ta kwashe fiye da shekaru 20 bata da tsayayyiyar gwamnati, inda kungiyoyi masu dauke da makamai ke ci gaba da kara kaina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.