Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya kaddamar da yakin neman Zabensa a Faransa

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya kaddamar da yakin neman zaben shi a karon farko a gaban dubun dubatar Faransawa a birnin Marseille bayan bayyana aniyar yin Tazarce akan madafan iko . Shugaban yace ya dauki matakan karya abokin hamayyarsa Francois Hollande na Jam’iyyar Gurguzu.

Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa lokacin da yake kaddamar da yakin neman zabensa wa'adi na biyu à birnin Marseillea ranar 19 ga watan Fabrairu
Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa lokacin da yake kaddamar da yakin neman zabensa wa'adi na biyu à birnin Marseillea ranar 19 ga watan Fabrairu REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Dubban magoya bayan shugaban ne sun ke ta yin tafi, lokacin da Mista Sarkozy yake caccakar Babban abokin adawar shi Francois Hollade, yayin gangamin da aka yi a wani dakin taro da ke birnin Marseille.

Fiye da magoya baya dubu goma ne suka halarci gangamin da shugaban ya yi amfani da shi wajen kiran faransawa su hada hannu, domin kayar da wadanda ya kira, masu tsammanin shan kaye a zaben mai zuwa.

Sai dai wannan na zuwa ne Yayin da Francois Hallade na jama’iyyar Socialist, ke gaba da Shugaba Sarkzy a kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta baya bayan nan da aka gudanar, a daidai lokacin da ya rage saura makonni tara a gudanar da zaben shugaban kasa.

Kwanaki hudu da bayyana aniyar shi ta yin tazarce, Faransawa suka haddace jigon yakin neman zaben Sarkozy, wadanda suka hada da yaki da auren jinsi guda, bai wa baki damar yin zabe, rage kasafin kudi da bunkasa makamashin Nukiliya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.