Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy yace yafi dacewa ya jagoranci Faransawa

Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, yace shi ya fi dacewa ya jagoranci kasar, bayan bayyana kudirin yin Tazarce a saman madafan iko watanni uku a gudanar da zaben shugaban kasa duk da zaben jin ra’ayin Faransawa ya nuna abokin hamayyarsa ne Francois Hollande na jam’iyyar Socialist akan gaba.

Shuagaban Faransa Nicolas Sarkozy.
Shuagaban Faransa Nicolas Sarkozy. AFP PHOTO / THOMAS COEX
Talla

Sarkozy ya danganta kansa a matsayin wanda ya dace da Faransa a dai dai lokacin da kasar ke cikin rudanin Tattalin arziki amma kuma Shugaban ya yi suka ga abokin karawarsa Francois Hollande inda ya kira shi a matsayin mai mafarki.

A wata hira da kafar Telebijin din kasar Faransa, Shugaba Sarkozy yace ya kudurta yin tazarce ne saboda halin da Faransa da Turai da Duniya ke ciki inda yace rashin yin tazarce kamar haramta ma kansa ne yin abun da ya dace.
Sarkozy ya soki yakin neman zaben Hollande wanda yace zai samar wa dubun dubatar ‘yan kasar aikin karantarwa.

Wani zaben Ra’ayin Faransawa da aka gudanar ya nuna Shugaba Sarkozy zai sha kaye a zabe zagaye na biyu da za’a gudanar a watan Mayu, sai dai har yanzu Sarkozy yana da Kwarin gwiwa game da tsare tsare shi da suka kawo shi saman mulki a shekarar 2007.

Yanzu haka dai Sarkozy ya kaddamar da yakin neman zaben shi ne ta hanyar zamani inda ya bude sahfin zumunta na Twitter a ranar bayyana yin tazarce.

Tun shekarar 1988 rabon Jam’iyyar gurguzu ta socialist da lashe zaben shugaban kasa amma a bana dan takarar Jam’iyyar Hollande, mai shekaru 57 na haihuwa yana da rinjayen kuri’u a zaben jin ra’ayin Jama’a

Wani sakamakon zaben Jin ra’ayin na baya bayan nan da aka gudanar ya nuna cewa Hollande zai lashe zagayen farko da yawan kuri’u kashi 28, Sarkozy kuma zai samu yawan kuri’u kashi 24 wanda zai bada damar zuwa zagaye na biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.