Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande yace zai samar da sauyi a Faransa

Watanni uku ya rage Faransawa su gudanar da zaben shugaban kasa, amma dan takarar jama’iyyar Socialist, Francois Hollande ya lashi takobin samar da sauyi a kasar, a lokacin yak e kaddamar da yakin neman zabensa.

François Hollande, le candidat socialiste à la prochaine élection présidentielle, lors de  son grand oral au Bourget, le 22 janvier 2012.
François Hollande, le candidat socialiste à la prochaine élection présidentielle, lors de son grand oral au Bourget, le 22 janvier 2012. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Francois Halland, Mai shekaru 57, ya dude kalaman nashi da cewa yana sane da nauyi da aka dora mishi na ganin an samar da sauyi, ta hanyar ganin jama’iyyarsu ta ‘yan gurguzu ta lashe zaben da za’a gudanar.

A jawabinsa ga ‘ya‘yan jama’iyyarsu kusan dubu 25, Mista Hollande yace a shirye yake ya kalubanci shugaba Sarkozy.

Hollande ya yi wa magaoya bayan shi jawabi kan yadda ya taso a Mahaifar shi ta Normandy, a gaban iyayen shi masu ra’ayin mazan jiya, kuma ya yi godiya ga iyayen shi da suka bashi damar zaben tsari irin na gurguzu.

Dan takarar ya tabo batun sojan Faransa da ke Aghanistan, tare da nuna takaicin shi game da yadda aka hallaka mutane hudu daga cikinsu a ranar Juma’a, inda yace lokaci ya yi da faransa zata shaidawa duniya kammala aikinta a Aghanistan, yace zai tabbatar da cewa dakarun faransa basu wuce shekara ta 2012 a Afghanistan ba.

A wani zaben jin ra’ayin jama’a da aka gudanar Hollande ne akan gaban shugaba Sarkozy da rinjayen kuri’u kashi 28 zuwa 30 cikin 100, Shugaba Sarkozy kuma ya samu kashi 23 zuwa 24 cikin 100.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.