Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy ya kwarmata kudirin yin tazarce a Faransa

Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya kwarmata shirin yin tazarce a zaben shugaban kasa da za’a yi a watan Afrilu, bayan an dade ana rade radin tsayawar shugaban takara. Sai dai shugaban bai fito fili ya bayyana kudirin yin takarar ba. 

Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa, a lokacin da yake jawabi da wata kafar Telebijin a kasar Faransa
Nicolas Sarkozy Shugaban kasar Faransa, a lokacin da yake jawabi da wata kafar Telebijin a kasar Faransa REUTERS/France Televisio
Talla

A wata hira da ya yi da manema labarai, shugaba Sarkozy yace, akwai alkawari tsakanin shi da Faransawa, saboda haka babu yadda zai gudu ba tare da cika alkawalin ba, wajen kokarin magance matsalolin da ke addabar kasar da suka hada da tattalin arziki

Shugaban ya bayyana Karin kudin haraji daga sama da kashi daya da rabi, zuwa sama da kashi 21, wanda ake saran zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Octoba mai zuwa.

Shugaba Sarkozy wanda ya kudurta farfado da darajar tattalin arzikin Faransa, yanzu haka akwai kalubalen magance matsalar rashin aikin yi a kasar da dimbim basukan da ake bin Faransa.

Wannan fitowar ta Sarkozy na zuwa ne mako guda bayan abokin hamayyarsa Hollande ya kaddamar da yakin neman zabensa inda ya yi kakkausar suka ga matakan da shugaban ya dauka wajen warware matsalar tattalin arziki.

Wani zaben jin ra’ayin Jama’a da aka gudanar ya nuna Hollande ne zai lashe zaben shugaban kasa da rinjayen kuri’u kashi 56 cikin 100 inda kuma Sarkozy ya samu kuri’u kashi 44.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.