Isa ga babban shafi
Faransa

Cantona, tsohon dan wasan Manchester zai shiga takarar shugaban kasar Faransa

Wata Jarida a kasar Faransa ta ruwaito tsohon dan wasan kwallon kafar kasar Eric Cantona, zai shiga takarar shigabancin kasa domin kalubalantar Sarkozy. Kuma Jaridar tace ta samu wasikar da ya aikawa masu mulkin yankunan kasar domin ba shi goyon baya.

'Eric Cantona a lokacin da yake hira da wata kafar yada Labarai
'Eric Cantona a lokacin da yake hira da wata kafar yada Labarai www.bankrun2010.com
Talla

Jaridar Liberation ta wallafa wasikar da Tsohon dan wasan mai shekaru 45 ya rubuta domin neman goyon bayan Faransawa tsayawa takarar shugaban kasa.

A shekarar 2010 Cantona ya mamaye kafafen yada labarai inda ya bukaci ‘yan kasar janye kudadensu daga bankuna domin gurgunta bankunan a mastsayin wani juyin juya hali.

Cantona wanda ake wa kirarin Sarki Eric yana daga cikin fitattun ‘yan wasa a Tarihin Manchester United inda ya taka kwallo daga shekarar 1992 zuwa 1997.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.