Isa ga babban shafi
Faransa

Dominique de Villepin ya bayyana shirin kalubalantar Sarkozy a zabe

Tsohon shugaban kasar Faransa Dominique de Villepin ya bada sanarwar tsayawa takara domin kalubalantar Shugaban kasar Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a watan Mayun badi, yace zai tsaya takara ne domin kare wasu bukatun Faransa.

Tsohon shugaban kasar Faransa Dominique de Villepin
Tsohon shugaban kasar Faransa Dominique de Villepin REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Dominique de Villepin, an haife shi ne a shekarar 1953, a kasar Morocco, wanda ke karkashin Faransa a wancan lokaci.

Fasahar da Allah Ya bashi, ya sa wasu na masa kallon mai ji da kai, yayin da wasu kuma ke girmama shi.

Ya fara aikin diflomasiyarsa a shekarar 1980, a kasashen India da Amurka.

De Villepin ya zama babban hafsa a fadar shugaban kasa, Jacque Chirac a shekarar 1995, daga baya kuma ya zama ministan cikin gida da kuma Fira Minista daga shekarar 2002 zuwa 2007.

A bara, an wanke shi daga zargin almundahana a wata badakalar kwangila, abinda ya zafafa gabarsa da shugaba Nicolas Sarkozy.

A cikin wannan shekarar ya kafa wata kungiyar siyasa, yanzu kuma ya bayyana shirin kalubalantar Sarkozy a zabe mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.