Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Sarkozy ya bukaci hada kan Faransa da Jamus don magance matsalar Turai

Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, ya bayyana cewar, ya zama dole ga kasashen Faransa da Jamus su hada kai, don magance matsalar da ke addabar kasashen Turai.

Lokacin da Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya kai ziyara birnin  Toulon
Lokacin da Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya kai ziyara birnin Toulon Reuters
Talla

A wani gagarumin jawabi da ya yi jiya a garin Toulon, shugaban ya yaba da juriyar da ‘Yan kasar Faransa ke nunawa, kan kuncin da suke fuskanta, inda yake cewa, ya zama dole kowa ya bada gudummawa don ceto kasar da kuma Yankin Turai.

Sarkozy ya kuma yi gargadin cewar, wannan matsala zata dauki dogon lokaci, da kuma wahala kafin a shawo kanta, inda ya kara da cewa Faransa ba za ta bada kai bori ya hau ba.

Shugaban yace, zasu ci gaba da kare martabar kudin Euro, kuma zasu kalubalanci wadanda ke da shakku kan kudin, da kuma fatar ganin ya karye.

A cewarsa, Faransa na yaki ne domin ganin cewar, kungiyar kasashen Turai ta ci gaba inda ya bukaci sake ganawa da shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ranar litinin, don shata wani sabon daftarin da zai kare makomar Yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.