Isa ga babban shafi
S&P-Turai

S&P ya yi barazanar rage darajar iya biyan bashin kasashen turai

Kamfanin da ke sa ido kan tattalin arzikin kasashen duniya, na Standard and Poors, ya yi barazanar rage darajar iya biyan basukan kasashen turai 17 da ke anfani da kudin Euro da suka hada da Faransa da Jamus, saboda abinda Kamfanin ya kira fargabar matsalar bashin da ke addabar Yankin.

Alamar danja ga kasashen Turai kusa da tambarinsu
Alamar danja ga kasashen Turai kusa da tambarinsu REUTERS/Yves Herman
Talla

Wannan barazana na zuwa ne sa’oi kadan bayan amincewa da sabbin matakai da shugabanin kasashen Faransa da Jamus suka yi a tsakaninsu, kafin taron kasashen Turai ranar juma’a, inda kanfanin yace ana iya rage darajar basukan manyan kasashen da suka hada da Jamus da Faransa da Austria da Holland da Finland da Luxembourg, daga mataki na uku, zuwa mataki na biyu cikin watanni uku masu zuwa.

Sai dai shugaban kasar Faransa da Angela Merkel ta Jamus sun sabon tsarin da suka amince da shi ya shafi hukunci ga kasashen da suka saba wajen datse kasafin kudadensu domin kaddamar da hanyoyin ceto kudin euro.

Shugaban kasar Faransa Sarkozy ya bukaci a cim ma matsayar yarjejeniyar a watan Mayun badi tare da tsayar da lokacin sasantawa bayan kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisu kasar a watan Yuni.

Sai dai kamfanin S&P yace zai cim ma bincikensa cikin lokacin kalilan domin kimanta girman iya biyan bashin kasashen.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.