Isa ga babban shafi
Italiya

Italiya ta fara shirin daukar matakan tsuke bakin aljihu

Kasar Italiya da ke fama da matsalar tabarbarewar tattalin arziki ta fara shirin daukar tsauraran matakan tsuke bakin aljihun gwamnati, domin ceto darajar kudin euro inda za’a gabatar da sabbin tsare tsaren a gaban Majalisar kasar a yau Litinin.

Fira Ministan Italiya Mario Monti a Zauren Majalisar Dattawan kasar
Fira Ministan Italiya Mario Monti a Zauren Majalisar Dattawan kasar Reuters/Remo Casilli
Talla

Tuni dai Majalisar zartarwa kasar ta amince da wasu jerin sabbin matakan karin haraji da rage kashe kudaden gwamnati.

Ana sa ran Fira Ministan kasar Mario Monti, zai gabatar da shirin tsuke bakin aljihun a gaban Majalisar dokokin kasar a yau Litinin.

A Lokacin da Fira Ministan ke jawabi ga kungiyoyin kwadago ya ce gwamnati ta samu karin kwarin gwiwa daga shugaban kasa da majalisar dokoki, a kan hurumin daukar tsauraran matakai, da za su taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

A yau ne kuma shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da Angela Merkel zasu gana a birnin Paris domin cim ma matsaya ga sabbin tsare-tsaren da zasu ceto darajar kudin euro.

Watanni uku ke nan da Mario Monti ya karbi ragamar shugabanci daga hannun Silvio Berlusconi wanda ya sauka saboda fargaba da tabarbarewar kasuwar kudaden kasar, amma yanzu haka Monti yace kasar Italiya na cikin wani mawuyacin halin tattalin arziki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.