Isa ga babban shafi
Italiya

Monti zai sake fuskantar kuri’a a karamar majalisar Italiya

Sabon Fira Ministan Italiya Mario Monti zai sake fuskantar kuri’ar yankan kauna a karamar Majalisar kasar bayan tsallake siradin kuri’ar a babbar majalisa kan sabbin tsare tsarensa domin kawo karshen rikicin tattalin arzikin kasar.Mista Monti ya samu kuri’ar amincewa a majalisar dattawan kasar, inda zai gaggauta aiwatar da sauye sauyen da za su taimaka wajen samar da ci gaban tattalin arziki.shugabannin faransa Nickolas Sarkozy ya amince da tsare tsaren sabon Fira Ministan, da ake sa ran zasu taimaka wajen kaucewa yaduwar matsallar bashi ga sauran kasashen Turai.Sai dai majalisar wakilan kasar ma za ta kada irin wannan kuri’ar a yau juma’a, kuma ana has ashen Monti zai sake samun nasara a karamar Majalisar.Monti ya ba ‘yan kasar tabbacin cewar wasu daga kasashen waje basu da hurumin juya akalar tattalin arzikin kasar, ita ma shugabar gwamnatin Jamus, Angela Markel ta bashi tabbacin goyon baya.  

Fira Ministan Italiya Mario Monti a Zauren Majalisar Dattawan kasar
Fira Ministan Italiya Mario Monti a Zauren Majalisar Dattawan kasar Reuters/Tony Gentile
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.