Isa ga babban shafi
Girka

Kungiyoyin Ma'aikata na Girka sun nuna rashin jin dadi kan tsuke bakin aljuhu

Kungiyoyin Maaikata na kasar Girka yau Talata, sun nemi mutanen kasar da su fito domin wani zagayen zanga-zangan ranar daya ga watan gobe na Disamba, domin nuna rashin jin dadi game da matakan tsuke bakin aljihu da sabuwar Gwamnatin kasar ta fito dasu.

Preme Ministan Lucas Papademos na kasar Girka
Preme Ministan Lucas Papademos na kasar Girka Reuters / Yannis Behrakis
Talla

Cikin wata sanarwa Kungiyoyin sun fadi cewa sam ba zata sabu ba, tsarin matakan kowa yaji ta a jika, kamar yadda sabuwar Gwamnatin ta tsara cikin kasafin kudinta na shekara mai zuwa ta 2012.

Masu bin kasar bashi, da kungiyar Tarayyar Turai da Asusun Bada lamuni na Duniya, IMF, sun ce ala tilas sai kasar ta aiwatar da tsarin kasafin kudin kafin a basu rancen Kudin Turai Euro billiyon 8, domin fita daga halin ni ‘yasu.

Sabon Prime Ministan kasar ta Girka Lucas Papademos ya na shirin ganawa da sabon Shugaban Babban Bankin Turai, Mario Draghi, cikin matakan da ake dauka na shawo kan matsalolin da kasar ke ciki na tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.