Isa ga babban shafi
Girka

Sabon Fira Ministan Girka zai fuskanci kalubalen aiwatar da sauye-sauye

Yau Juma’a ne ake saran rantsar da sabon Fira Ministan kasar Girka, Lucas Papademos, wanda zai fuskanci kalubalen aiwatar da sauye sauye da kuma tsuke bakin aljihun Gwamnati.An zabi Papademos ne mai shekaru 64 na haihuwa a matsayin sabon Fira Minista domin biyan bukatun kasashen Turai da hukumar bada Lamuni domin kammala sabon tsarin da tsohuwar gwamnatin Jam’iyyar Socialist ta yi alkawli.Papademos shi zai jagoranci kafa sabuwar gwamnati da za’a daurawa alhakin farfado da darajar tattalin arzikin kasar.Zabensa na zuwa ne bayan kwashe kwanaki hudu ana muhawara tsakanin manyan Jam’iyyun siyasar kasar, Jam’iyyar Gurguzu ta Socialist da Jam’iyyar adawa ta Conservatives bayan Fira Ministan kasar George Papandreou ya yi murabus.An daurawa sabuwar gwamnatin alhakin gudanar da zabe idan har Girka ta cim ma Yarjejeniya tsakaninta da kungiyar Tarayyar Turai a Majalisar kasar da hada Jam’iyyar PASOK ta Gurguzu da Jam’iyyar LAOS wadanda suke da mataimaka 254 cikin kujeru 300 a majalisar.  

Lucas Papademos sabon Fira Ministan kasar Girka
Lucas Papademos sabon Fira Ministan kasar Girka AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.