Isa ga babban shafi
Girka

An fara Yajin aiki kwanaki biyu a kasar Girka

An fara yajin aikin gama-gari na kwanaki biyu a kasar girka wanda ya shafi hana tashi da saukar jiragen sama tare da rufe masana’antu da ofisoshin ma’aikata a cikin kasar.Yajin aikin na kwanaki biyu na zuwa ne kafin  Majalisar kasar ta amince da wani sabon matakin tsuke bakin aljihu wanda ya hada da Karin kudaden haraji da katsewar rashin aikin yi.Rahotanni na nuni da cewa, akalla ‘Yan Jaridu 2,000 suka gudanar da zanga-zanga a birnin Athens, domin nuna adawa da matakin shirin rage ma’aikata.Manyan kungiyoyin kwadagon kasar guda biyu da suka hada da kungiyoyin ma’aikatan gwamnati da na ‘yan kasuwa ne suka kira yajin aikin wanda za’a kwashe tsakanin yau Laraba zuwa Alhamis ana gudanarwa. 

Masu gudanar da zanga-zanga a birnin Athens na kasar Girka
Masu gudanar da zanga-zanga a birnin Athens na kasar Girka REUTERS/Yannis Behrakis
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.