Isa ga babban shafi
IMF

Akwai Yuwuwar Hukumar IMF ta Tallafa wa kasar Girka

Hukumar Bada lamuni ta duniya, ta na tunanin baiwa kasar Girka Karin tallafin Dala bilyan 13, bayan Dala bilyan 18 da hukumar ta baiwa kasar a baya.Rahotanni sun ce, yanzu haka ana cigaba da tattaunawa kan lamarin, a dai dai lokacin da shugaban Hukumar Bada lamini, Dominique Strauss Khan ke cewa, Girka ta na fuskantar mawuyacin hali.A wani labarin, shugaban gudanarwar kungiyar kasashen Turai, Herman Van Rompuy, ya ce za’a gudanar da taron shugabanin Gwamnatocin kasashen, a watan gobe, domin nazarin halin da kasar ta Girka ke ciki.Yayin da yake jawabi a kasar Japan, Rompuy ya ce a matsayin sa na shugaban kungiyar, zai kira taron shugabani tare da daukar sabbin matakan magnace matsalar.Tuni aka samu faduwar Hannayen jari a kasashen Turai da Asiya, bayan kanfanin dake kula da hada hadar hannayen jarin, ya bada rahotan cewar, matsalar kasar Girka ka iya yaduwa zuwa wasu kasashen Turai, musamman kasar Portugal.Hannayen jari a London, sun fadi da sama da kashi biyu da rabi, kamar yadda suka fadi a Jamus, yayin da hannayen jarin suka fadi da kusan kashi hudu a Faransa.A kasashen Portugal da Girka, hannayen jarin sun fadi da kashi shida cikin 100.

Le directeur général du Fonds monétaire international, Dominique Strauss-Kahn, demande à la communauté internationale de maintenir ses aides.
Le directeur général du Fonds monétaire international, Dominique Strauss-Kahn, demande à la communauté internationale de maintenir ses aides. (Photo : Reuters)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.