Isa ga babban shafi
Girka

‘Yan sanda sun tarwatsa gungun masu zanga a kasar Girka

‘Yan sandan kwantar da tarzoma a kasar Girka sun watsa hayaki mai sa hawaye kan matasa masu zanga-zangar nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamanatin kasar.An yi irin wannan zanga zangar a kasashen Italiya da Spain.‘Yan sandan sun ce a kalla matasa dubu Ashirin da bakwai da suka lullube fuskokinsu, ke gudanar da zanga-zangar a birnin Athens, inda wasu dubu 15 ke gudanar da tasu a Thessalonica, wanda shine birni na 2 mafi girma a kasar ta girka. 

Masu gudanar da zanga-zanga a birnin Athens na kasar Girka
Masu gudanar da zanga-zanga a birnin Athens na kasar Girka REUTERS/Yannis Behrakis
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.