Isa ga babban shafi
France

Faransa Ta Haramtawa Mata Sa Niqabi

Karamar majalisar kasar Faransa ta zartas da doka da babban rinjaye na haramtawa mata musulmi amfani da lullubi ( niqabi) da mata ke sanyawa dake rufe ilahirin fuska.Wakilai 335 ne daga cikin wakilai 577 suka albarkaci dokan yau, jajibari kasaitaccen bukin Faransa na ranar Bastille.Wannan doka yanzu haka na kan hanyar zuwa majalisar Dattawan kasar watan jibi, to amma masu ja da dokar na ganin cewa mai yiwuwa ayi watsi da dokar kafin ta fara aiki, idan har ta kai ga Alkalan Kotun tsarin mulkin kasar.Yayin da matakin Shugaba Nicholas Sarkozy na haramta amfani da lullubi, na niqab ke samun karbuwa daga jamaa, wadanda basa son dokar na ganin danne hakkin dan Adam ne kawai.A yanzu haka akwai irin wadan nan dokoki da ake shirin zartaswa akasashen Belgium, Spaniya da Italiya. 

Mata cikin niqab
Mata cikin niqab rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.