Isa ga babban shafi

Babban kalubale na tunkaro tattalin arzikin kasashe masu arzikin man fetur- IMF

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya gargadi Najeriya da sauran kasashe masu arzikin man fetur a yankin kudu da Sahara, da su shirya fuskantar raguwar kudaden shiga a shekaru masu zuwa, sakamakon yadda kasashen duniya ke sauya akalarsu wajen dogaro ko amfani da albarkatun man fetur zuwa makamashi maras gurbata muhalli.

Shugaban asusun bada lamuni na Duniya IMF Kristalina Georgieva.
Shugaban asusun bada lamuni na Duniya IMF Kristalina Georgieva. REUTERS - Denis Balibouse
Talla

A cikin wani sabon rahoto mai taken "Tsimi da tanadin kudade daga harajin mai zai iya taimakawa kasashe masu arzikinsa a nahiyar Afirka," asusun na IMF ya ce kasashe masu fitar da mai a yankin kudu da Saharar Afirka ya kamata su rika adana kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na rarar kudaden shigar da su ke samu domin tunkarar rashin tabbas ko hawa da sukar farashin gangar danyen mai.

Rahoton tattalin arzikin yankin na baya-bayan nan na IMF ya nuna cewa farashin mai ya tashi daga faduwar da ya yi zuwa dalar Amurka 23 kan kowace ganga zuwa dala 120 a cikin shekaru biyun da suka gabata, wanda ya haifar da rashin tabbas na kudaden shiga ga tattalin arzikin kasashen da ya dogara da man fetur din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.