Isa ga babban shafi

Mafi munin kalubale na tunkarar tattalin arzikin duniya - IMF

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi gargadin cewa duniya za ta kara fuskantar mafi munin kalubale, yayin da ake ci gaba da yaki a Ukraine da kuma fama da hauhawar farashin kayayyaki.

Shugabar Asusun bada lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva .
Shugabar Asusun bada lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva . AP - Ludovic Marin
Talla

Kididdigar da IMF ya fitar na cewa, daga nan zuwa 2023 mutane da dama za sus amu koma bayan tattalin arziki.

Hukumar da ke aikin daidaita tattalin arzikin duniya, ta rage hasashen ci gaban tattalin arzikinta, sakamakon tasirin mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.

Ana sa ran tattalin arzikin Birtaniya zai ragu a shekara mai zuwa, bayan da aka samu karuwar kusan kashi 0.3.

Wannan ya nuna raguwar kashi 0.2% daga hasashen IMF na Yuli, da faduwa daga kashi 3.6% na habakar tattalin arzikin Birtaniya da ake tsammanin samu a shekarar 2022.

Asusun na IMF yana aiki don daidaita tattalin arzikin duniya kuma daya daga cikin manyan ayyukansa shine gaggawar tunkarar matsalolin da ke kokarin kawo tarnaki ga tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.