Isa ga babban shafi
Wasanni

Yadda manyan kungiyoyi suka gaza taɓuka abin kirki a gasar zakarun Turai ta 2022

Wallafawa ranar:

Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon tare da Khamis Saleh ya maida da hankali kan yadda manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai a bana suka gaza tabuka abin kirki a gasar zakarun Turai. A ranar Larabar da ta gabata ne aka kammala wasannin rukuni na gasar zakarun nahiyar Turai, inda aka samu kungiyoyi 16 da suka kai matakin zakaye na biyu a gasar.

Tambarin gasar zakarun Turai na UEFA
Tambarin gasar zakarun Turai na UEFA REUTERS/Jean Pierre Amet
Talla

Kungiyoyi 32 daga kasashe 15 na Turai ne suka fafata a matakin rukuni a bana, kuma daga cikin wancan adadi 16 sun fice daga gasar domin kuwa 8 sun koma gasar Europa 8 kuma suka koma gida.

Sai dai gasar ta bana tazo ne da wani abin mamaki ganin yadda manyan kungiyoyin da suka saba nisa a gasar a bana ta sauya zani, domin kuwa wasun su tun daga matakin rukuni aka fidda su lamarin da ya sa masharhanta da masu sha’awar wasan kwallon kafa a duniya ke ci gaba da mamakin rashin tabuka abin kirki na manyan club club din.

Daga cikin irin wadannan kungiyiyi akwai Atlatiko Madrid da Barcelona da Juventus da Sevilla da Ajex da dai sauran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.