Isa ga babban shafi
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Kan zargin badakalar da aka samu tsohon shugaban babban bankin Najeriya da ita

Wallafawa ranar:

Maudu’in na wannan rana ya mayar da hankali ne, kan rahoton da kwamitin shugaban Najeriya ya fitar game da badakalar da aka samu tsohon shugaban babban bankin kasar, Godwin Emefile, da aikatawa na bude asusun bankuna sama da 500 a kasashen waje.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kenan, Godwin Emefiele a gaban kotu, bisa zargin badakalar kudade.
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kenan, Godwin Emefiele a gaban kotu, bisa zargin badakalar kudade. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Sai dai, Godwin Emefiele, ya yi watsi da rahoton binciken da ya bayyana cewar ya bude asusun bankuna har guda 593, wadanda yayi amfani da su wajen boye makudaden kudaden gwamnati da niyyar yin kwanciyar magirbi akansu.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Emefiele, wanda aka bayar da belinsa a ranar Juma’a, ya ce tuni ya bai wa lauyoyinsa umarnin shigar da kara kan rahoton da yace babu abinda ya kunsa sai karairayi domin bata masa suna.

SHiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin da Nasiruddeen Muhammad ya gabatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.