Isa ga babban shafi

Emefiele ya musanta rahoton bude asusun bankuna 593 a kasashen waje

Tsohon shugaban babban bankin Najeriya Godwin Emefiele, ya yi watsi da rahoton binciken da ya bayyana cewar ya bude asusun bankuna har guda 593, wadanda yayi amfani da su wajen boye makudaden kudaden gwamnati da niyyar yin kwanciyar magirbi akansu.

Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele
Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Emefiele, wanda aka bayar da belinsa a ranar Juma’a, ya ce tuni ya bai wa lauyoyinsa umarnin shigar da kara kan rahoton da yace babu abinda ya kunsa sai karairayi domin bata masa suna.

Cikin rahoton binciken da ya shafe sama da watanni hudu yanayi, Jim Obazee da shugaba Bola Tinubu ya dorwa nauyin aikin, ya bayyana cewar tsohon gwamnan na CBN ya bude daruruwan asusun bankunan da ya gano, ba tare da izinin hukumar gudanarwar babban bankin ba, ko kuma na shugaban waccan lokaci wato Muhammadu Buhari.

Zalika rahoton ya kuma bayyana gano fam dubu 543 da 482 da Emefielen ya boye a asusun wasu bankuna da ke kasar Birtaniya kadai.

Wani batu da binciken kwamitin na musamman din ya gano kuma shi ne yadda ake tuhumar Godwin Emefiele da bin wasu haramtattun hanyoyi cikin dabara, wajen karbe ragamar jagorancin wasu bankuna a Najeriya, da suka hada da Union, da Keystone da kuma Polaris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.