Isa ga babban shafi

Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan bankin Najeriya

Kotu a Najeriya ta saki tsohon gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele daga gidan yarin Kuje bayan da ya cika sharuddan belinsa, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sharuddan belin da Emeifiele ya cika sun hada da ajiye naira miliyan 300, da mika dukkanin takardunsa na tafiye-tafiye, sai kuma gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.

Sakin tsohon gwamnan bankin Najeriyar ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan kasar da dama ke tofa albarkacin bakinsu kan sakamakon binciken da aka shafe sama da watanni hudu ana yi, inda mai bincike na musamman, Jim Obazee, ya bankado yadda Emefiele da wasu mutane suka sace makudan kuddade, wadanda suka boye a asusun bankunan kasashen waje guda 593 da suka bude ba tare da izinin shugaba Muhammadu Buhari ba, wanda ke mulki a waccan lokaci.

Rahoton da wasu majiyoyi suka ce tuni aka mika wa shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu a farkon watan nan na Disamba, ya bankado yadda tsohon gwamnan babban bankin yayi sama da fadi miliyoyin dalar Amurka, tafka almundahana a shirin sake fasalin kudin Najeriya da kuma ajiye fam miliyan 543 a asusun wani banki da ke Birtaniya.

Wani batu da binciken kwamitin na musamman din kuma ya gano, shi ne yadda ake tuhumar Godwin Emiefiele da bin wasu haramtattun hanyoyi cikin dabara, wajen karbe ragamar jagorancin wasu bankuna a Najeriya.

A  halin yanzu dai ‘yan Najeriyar na dakon fitar musu da rahoton tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon gwamnan bankin na CBN, da aka shafe sama da watanni hudu ana gudanar da bincike kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.