Isa ga babban shafi

EFCC ta kama tsohon ministan kula da wutar lantarkin Najeriya

Hukumar yaki da cin hanci da Rashawa EFCC, ta ce yanzu haka tsohon karamin ministan kula da lantarkin Najeriya Olu Agunloye na tsare a hannunta.

Wasu turakun samar da hasken wutar lantarki a Najeriya.
Wasu turakun samar da hasken wutar lantarki a Najeriya. REUTERS - Akintunde Akinleye
Talla

Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da hukumar ta shelanta neman tsohon ministan a zamanin gwamnatin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ruwa a jallo, bisa zarginsa da hannu a badakalar dala biliyan 6 da ake neman damfarar gwamnati ta hanyar fakewa da tsohon aikin tashar samar da wutar lantarki da Mambila.

Wata majiya ta bayyana cewar, Agunloye ya shiga hannu ne tun a ranar 13 ga watan nan na Disamba, sai dai ba a bayyana hakan ba a waccan lokaci.

Agunloye ya rike mukamin karamin ministan kula da lantarkin Najeriya ne daga shekarar 1999 zuwa 2003.

A makon da ya gabata ne kuma tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewar a shirye yake ya bayar da shaida ko a ina ne, akan zargin hannu a badakalar da ake yi wa tsohon ministan nasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.