Isa ga babban shafi

Tsarin demokradiyar kasashen Yamma bai dace da Afirka ba - Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa tsarin dimokaradiyyar kasashen Yamma bai dace da Afirka ba.

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olosegun Obasanjo, yayin wani taro a jihar Oyo.15/09/23
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olosegun Obasanjo, yayin wani taro a jihar Oyo.15/09/23 © Seyi Makinde X
Talla

Tsohon shugaban na Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce irin wannan dimokuradiyya ba ta yi la'akari da tarihi da al'adun nahiyar Afrika ba.

Obasanjo  ya ce dimokuradiyyar kasashen yammacin duniya ya gaza samar da ci gaba a nahiyar Afirka domin ba ta la'akari da ra'ayin mafi yawan jama'arta.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wani babban taron tuntuba da bita kan demokradiyar yammacin duniya ga Afirka a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yana mai bada shawarar bin tsarin demokradiyar Afirka tsan-tsa.

Obasanjo, wanda ya kira taron, ya bayyana dimokaradiyyar ‘yan sassaucin ra’ayi a yammacin turai a matsayin gwamnatin wasu tsirarun mutane amma ba daukacin jama’a ko yawan jama’a ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.