Shirin rayuwata a wannan rana ya duba shirye shiryen da alummar Najeriya ke yi na bikin karamar sallah wanda ke cigaba da karatowa a daidai lokacin nan da suke fama da halin matsi na rayuwa da hauhawar firashin kayakin abinci.
Bisa al'ada mutane kan dinka sabbin tufafi tare da dafa mabanbantan nau’ukan abinci dan rabawa makota da abokan arziki dan taya juna murnar bikin wannan rana, toh saidai a wannan karo, an samu babban gibi da sauyi game da yadda sallar ta riski iyalai.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Zainab Ibrahim.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu