Isa ga babban shafi
Rayuwata

Kan tukin ganganci da ya yi sanadiyyar rasa kafar wata daliba a Najeriya

Wallafawa ranar:

Shirin ya mayar da hankali kan halin da wata daliba ta shiga, sakamakon take ta da mota da wani matashi ya yi a Najeriya.

Daliba Fatima kenan da tukin gangancin wani matashi ya haifar mata da rashin kafa guda
Daliba Fatima kenan da tukin gangancin wani matashi ya haifar mata da rashin kafa guda © daily trust
Talla

Nema tare da samun ilimi wani abun farin ciki ne ga kowanne mahaluki, dalilin da ya sa makarantun zamani ke gudanar da bukukuwa domin taya ‘yan makaranta murna a yayin da suka kai wani mataki na kammala karatunsu, walau na firamare ko sakandare ko kuma gaba da haka.

Toh saidai a wannan karo, murna ta koma ciki a jihar Sokoton Najeriya, bayan wani dalibi, dan gidan masu hali, yayi sanadiyar gutsure wa wata daliba mai suna Fatima kafa saboda tukin ganganci da yayi a ranar da suka kammala zana jarabawarsu ta karshe a makaranta.

Tuni dai Kotu a jihar ta tura dalibin zaman wakafi na kwanaki 7 a gidan gyara hali saboda zargin da ake masa amma babu watawata kudi yayi halin shi, inda aka bada belinsa ba tare da ya fuskanci hukuncin da ya kamace shi ba.

Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin da Zainab Ibrahim ta shirya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.