Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Aisha Bashir kan yadda daliban Najeriya ke jiran a kwashe su daga Sudan

Wallafawa ranar:

Har yanzu daliban Najeriya na ci gaba da jiran tsammanin ganin an kwashe su daga Sudan, bayan da rundunonin soji masu rikici da juna suka sanar da tsagaita wuta da tsawon kwanaki uku, don baiwa jama’ar kasashen ketare damar ficewa daga kasar.

Wasu mazauna Sudan yayin kokarin ficewa daga kasar don gujewa fadan da ake gwabzawa tsakanin rundunonin dakarun kasar biyu.
Wasu mazauna Sudan yayin kokarin ficewa daga kasar don gujewa fadan da ake gwabzawa tsakanin rundunonin dakarun kasar biyu. REUTERS - EL TAYEB SIDDIG
Talla

 

Guda daga cikin daliban Najeriya da ke Sudan din Aisha Bashir Ahmad ta shaida wa Rukayya Abba Kabara cewa har zuwa misalin karfe biyar na yammacin ranar Talata, motoci basu je sansanin jami’ar da suka taru don kwashe su ba.

Dalibar ta ce lamarin ya haddasa musu galabaita, saboda yunwa, da kishirwa ba ya ga fargaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.